Dan Nageria Buhari Sunusi Ya Lashe Matsayi Na Uku a Gasar Alƙur’ani Ta Duniya a Saudiyya

Nasara ga Najeriya a Musabakar Alƙur’ani
Ɗan Najeriya, Buhari Sunusi daga Kano, ya samu nasarar zuwa matsayi na uku a gasar Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a Masallaci mai alfarma a Saudiyya.
Wannan nasara ta sanya Najeriya cikin farin ciki da alfahari, kasancewar gasar ta tattaro mahalarta daga ƙasashe 128.
Wanda Suka Yi Nasara
A wannan gasa, ɗan ƙasar Tchadi ya lashe matsayi na farko, yayin da ɗan Saudi Arabia ya tsaya na biyu. Wannan ya kara fito da gagarumar nasarar da ɗan Najeriya ya samu, duba da irin kalubalen da gasar ta ƙunsa.
Martanin Farfesa Mansur Ibrahim
Jagoran tawagar Najeriya, Farfesa Mansur Ibrahim daga Sokoto, ya bayyana godiya ga Allah bisa wannan nasara. Ya kuma jaddada cewa ainihin karramawa ba ta duniya ba ce, illa ta lahira ga waɗanda suka yi aiki da Alƙur’ani.
Ya yi kira ga Buhari Sunusi da sauran mahalarta su ci gaba da yin amfani da ilimin Alƙur’ani wajen inganta rayuwarsu, tare da neman yardar Allah.
Tarihin Buhari Sunusi
Rahotanni sun nuna cewa Buhari Sunusi ɗalibi ne mai hazaka da jajircewa wajen haddace Alƙur’ani. A shekarar 2024, ya lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Najeriya, wanda hakan ya ba shi damar wakiltar ƙasar a wannan gasa ta duniya a Saudiyya cikin shekarar 2025.
A jawabin da ya yi bayan samun nasarar, Buhari ya fara da miƙa godiya ga Allah, sannan ya gode wa malamansa da shugabannin da suka goyi bayansa har ya kai wannan matsayi.
Kyautar da Aka Baiwa Buhari
Shafin Ummi na Saudiyya ya ruwaito cewa an ba Buhari Sanusi kyautar Riyal 400,000, wanda ya kai kusan Naira miliyan 160 a kudin Najeriya.
Godiya da Kiraye-kiraye
Farfesa Mansur ya yaba da irin tallafin da gwamnatin tarayya, gwamnatin Kano da ta Zamfara suka bayar wajen horar da mahalarta.
Haka kuma ya nuna godiya ga Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto bisa rawar da take takawa a ci gaban musabakar.
Ya kuma yi kira da a baiwa Buhari Sanusi karramawa ta musamman a Najeriya, kamar yadda aka yi masa a Saudiyya.
Nasiha ga Musulmai
A gefe guda kuma, wani malamin Musulunci daga Sokoto, Dr Jabir Sani Mai Hula, ya yi kira ga al’umma su rika kula da yadda suke gudanar da sallah.
Ya bukaci Musulmi da su guji sanya tufafin da ke ɗauke da hotunan ’yan siyasa ko ’yan kwallo yayin yin ibada.
Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen tsare martabar sallah da kuma bayar da girmamawa ga wannan ibada mai daraja.