KannyWood

HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA JIHAR KANO TA DAKATAR DA MAWAKI SOJA BOY DA WASU JARUMAN MATA BIYU DAGA HARKOKIN FIM

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ta samu korafe-korafe masu yawa daga malamai da al’ummar jihar Kano kan bidiyon da ke nuna mawakin.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayar da umarnin cewa a ƙi tace duk wani fim ko waƙa da mawakin ko jaruman uku suka fito a ciki.

Jihar Kano – Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta ce ta samu korafe-korafe masu yawa a kan mawaki Usman Soja Boy saboda yawaitar batsa a bidiyon wakokinsa. Wannan ya sa hukumar ta dakatar da mawakin da wasu jarumai mata da aka gani a faifan bidiyon wakokinsa da ya ke saki a shafukan sada zumunta kwanan nan.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa dakatarwar na kunshe a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar ga manema labarai a Kano.

HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA HUKUNTA SOJA BOY

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta tabbatar cewa an kwace lasisin Soja Boy da wasu ‘yan Kannywood mata biyu da aka gani a bidiyon batsa.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya umarci sashen tace fina-finai na hukumar kada ya kuma tace duk wani fim ko waƙa da Soja Boy ko matan suka fito a ciki.

Abdullahi Sani Sulaiman ya ce:

“Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-Mustapha a yau ta dakatar da mawaki Usman, wanda aka fi sani da Soja Boy, biyo bayan korafe-korafen da mu ka samu daga al’ummar jihar Kano dangane da wani sabon salon bidiyo da ya dauko a wakokinsa.”

MALAMAI SUN YI KORAFI A KAN SOJA BOY

Jami’in hulda da jama’a na hukumar tace fina-finai ta Kano ya ce malamai da sauran jama’a sun yi takaicin yadda Soja Boy ya ke gurbata tarbiyyar jama’a.
A sababbin bidiyon mawakin da ya karade kafafen sada zumunta, ana ganin Soja Boy da jarumai Shamsiyya Muhammad da Hassana Suzan su na rungume juna, wanda ya saba da koyarwar Musulunci.

HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA GARGADI ‘YAN FIM

Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya gargadi ‘yan fim da su kaucewa duk wani abu da zai zubar masu da mutunci, musamman wanda ya saba addini.

Hukumar ta ce:

“Kafin ta dauki irin wannan matakin, hukumar na yin iya kokarinta kan gargadin masu irin wannan halayya da su kiyayi yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko ta sana’arsu.”

Hukumar ta ƙara da cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai taba addini, al’ada, ko tarbiyar al’ummar jihar Kano ba, ko da a sunan sana’a ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button