Najeriya Ta Dage Kan Haramcin Gwajin Makaman Nukiliya – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Najeriya tana nan daram kan matsayinta na haramta gwajin makaman nukiliya a duniya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar Hukumar CTBTO – wato hukumar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya – ƙarƙashin jagorancin sakatareta, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shettima ya ce Najeriya, kamar sauran ƙasashen Afirka da dama, na fuskantar manyan ƙalubale na tattalin arziƙi da zamantakewa. Ya lissafa su da suka haɗa da talauci, fatara, da sauyin yanayi.
A cewarsa, abun da ya fi kamata ƙasashen Afirka su mayar da hankali a kai shine magance matsalolin da ke barazana ga rayuwar al’umma, ba wai mallakar makaman nukiliya ba.
A nasa jawabin, Dr Robert Floyd ya jinjinawa ƙoƙarin Najeriya wajen aiwatar da manufofin hukumar CTBTO.
Ya kuma yaba da irin gudummawar da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ke bayarwa, domin rage gwajin makaman nukiliya a duniya.
✅ Wannan labarin yana daga cikin manufofin zaman lafiya da kariyar bil’adama. Karanta ƙarin labarai irin waɗannan a shafinmu.
© NgHausa.com.ng – Labarai na gaskiya, cikin sauƙi.