KannyWood

Baba Karami “Ban Yi Nadamar Shiga Harkar Fim Ba”

Tsohon shugaban ƙasa na ƙungiyar AFMAN (Arewa Film Makers Association of Nigeria), kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Alhaji Abdullahi Sani da aka fi sani da Baba Karami, ya musanta wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta.

A cikin wani bayani da ya yi wa mujallar fim, Baba Karami ya bayyana cewa labarin da ke cewa yana cikin wani hali na rashin lafiya tare da nadamar shiga harkar fim ba gaskiya ba ne.

“Ban taɓa cewa na yi nadama ba. Ban yi wa kowa ko wata kafar labarai irin wannan magana ba. Wasu ne kawai suka ƙirƙiri wannan labari domin biyan bukatunsu na kansu,” in ji shi.

Asalin Hoton Da Ake Yadawa

Baba Ƙarami ya bayyana cewa hoton da ake yadawa a kafafen sada zumunta—inda aka nuna shi a kan keken marasa ƙafa—ba hoton rayuwarsa ta gaskiya ba ne.

“An ɗauki hoton ne daga wani shirin fim da na fito a ciki, mai suna ‘Aliyah’. Ba hoton yadda nake a gaskiya ba ne, hoton fim ne kawai.”

Halin Lafiyarsa Yanzu

A bangaren lafiyarsa, jarumin ya tabbatar da cewa ya sha fama da ciwon hawan jini a kwanakin baya, har ma ya kwanta a asibiti, amma yanzu ya ce ya samu sauƙi sosai.

“Ina ci gaba da gudanar da ayyukana na yau da kullum. Gaskiya na samu sauƙi sosai,” in ji Baba Ƙarami.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks