Tarihin Fara Maulidi: Yaushe aka fara Mauludi kuma waye ya fara yinsa?

Tarihin Fara Maulidi: Me Malamai Suke Cewa?
Batun lokacin da aka fara yin Maulidi na ɗaya daga cikin muhawarorin da aka jima ana tattaunawa a kai.
Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Najeriya, ya bayyana cewa an fara yin Maulidi tun hijira ta 604. Ya ce Sarkin Erbil na lokacin, Mozaffar ad-Din, shi ne ya fara gudanar da shi. Wannan birnin yana cikin ƙasar Iraƙi a yau.
Ra’ayoyin Malamai
A cewar Sheikh Maraya, akwai malaman da ke soki taron Maulidi suna masu hujjar cewa Annabi Muhammadu (SAW) da Sahabbansa ba su taba gudanar da shi ba.
Sai dai ya jaddada cewa babu inda aka ambata a Alƙur’ani ko Hadisi ko kuma Ijma’in malamai cewa dole sai Annabi ya yi wani abu kafin ya halatta.
Abin Lura
Sheikh Maraya ya yi karin haske da cewa:
- Babban abin da ake dubawa shi ne ko Allah ya hana.
- Ko Annabi (SAW) ya haramta.
Idan ba haka ba, to ba za a ce an hana yin abu ba.
Ya tunatar da ayar Qur’ani wadda ke cewa:
“Abin da Manzon Allah ya kawo muku ku riƙe shi, abin da kuma ya hanaku ku guje masa.”