• Latest
  • Trending
  • All
Jerin Fina-Finan da Suka Yi Tashe a Kannywood 2024

Jerin Fina-Finan da Suka Yi Tashe a Kannywood 2024

December 26, 2024
Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai

Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai

November 21, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai

November 21, 2025
Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai

November 21, 2025
Nnamdi Kanu Ya Amince Zai Tuntubi Lauyoyinsa Kafin Ya Fara Kare Kansa

Kotun Tarayya Ta Ci Gaba da Shari’ar Nnamdi Kanu Ba Tare da Shi Ba Bayan Zargin Rashin Ladabi

November 20, 2025
ASUU Benin Ta Karyata Sabon Ƙarin Albashi: “Ba Zai Hana Ƙaurawar Malamai Ba

ASUU Benin Ta Karyata Sabon Ƙarin Albashi: “Ba Zai Hana Ƙaurawar Malamai Ba

November 20, 2025
NELFUND Za Ta Fadada Lamunin Dalibai Zuwa Sana’o’i da Fasaha a Najeriya

NELFUND Za Ta Fadada Lamunin Dalibai Zuwa Sana’o’i da Fasaha a Najeriya

November 17, 2025
Willie Obiano Yana Raye Cikin Koshin Lafiya a Amurka – An Karyata Jita-Jitar Mutuwarsa

Willie Obiano Yana Raye Cikin Koshin Lafiya a Amurka – An Karyata Jita-Jitar Mutuwarsa

November 15, 2025
Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe

Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe

November 13, 2025
Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike

Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike

November 12, 2025
Matsalar Tsaro a Kano: 'Yan sa kai na ƙauyen Shanono suna sintiri domin kare al’umma daga harin ƴan bindiga.

Matsalar Tsaro a Kano: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Faruruwa, Sun Yi Garkuwa da Mata Biyar

November 12, 2025
NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025

NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025

November 11, 2025
Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

November 11, 2025
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
Tuesday, December 2, 2025
NgHausa News
  • Login
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
No Result
View All Result
NgHausa News
No Result
View All Result
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
🚀 Join Our Telegram Community

Jerin Fina-Finan da Suka Yi Tashe a Kannywood 2024

by NgHausa
December 26, 2024
in KannyWood
0
Jerin Fina-Finan da Suka Yi Tashe a Kannywood 2024
0
SHARES
110
VIEWS

A cikin masana’antar Kannywood, ana samun sauye-sauye sosai, musamman a bangaren shirya fina-finai da kuma yadda ake gudanar da kasuwancinsu. Daga amfani da CD, an koma sinima, daga bisani kuma aka koma zuwa YouTube. Yanzu haka, ana ta kokarin shiga manhajojin duniya domin kara bunkasa harkar fina-finan Hausa.

A shekarar 2024, kamar yadda aka saba kowace shekara, masu shirya fina-finan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsara da kuma samar da fina-finai masu kayatarwa, wadanda suka burge masu kallo.

Tun bayan da aka koma dora fina-finai a kan YouTube, masana’antar Kannywood ta fara farfadowa, bayan durkushewar da ta yi a baya. Wannan sauyin ya sanya wasu manyan gidajen watsa labarai, kamar BBC, suka tankaɗe suka zaƙulo wasu daga cikin fina-finan da suka yi tashe a shekarar 2024.

Sai dai, fina-finan da suka yi fice a bana kusan duk suna cikin nau’in fina-finan dogon zango, wanda hakan ke nuna yadda masana’antar ke sauyawa da kuma hanyar da ta dosa domin samun dorewa.

Da farko, lokacin da aka fara shirya fina-finan dogon zango, wasu suna ganin ƙananan masu shirya fim ne kawai suke yin su domin dora su a YouTube, kuma ana ganin ba su da inganci. Amma a halin yanzu, manyan furodusoshi sun shiga wannan harkar sosai, suna kuma samun karbuwa.

See also  Maishadda: “Burin da nake da shi yanzu shi ne na fitar da Kannywood zuwa duniya!”

Jerin Fina-finan da Suka Yi Tashe a 2024:

  1. Labarina

Labarina fim ne mai dogon zango wanda fitaccen darakta Malam Aminu Saira ya shirya. Fim ɗin yana ɗauke da tsarin labari mai ban sha’awa, wanda ke amfani da dabarar zuba labarai daban-daban cikin babban labari guda. Wannan ya taimaka wajen tsawaita darajarsa ba tare da ya gundura masu kallo ba.

Fim ɗin ya fara fitowa tun shekarar 2020, inda aka fara da labarin Sumayya (Nafisa Abdullahi), daga baya ta rikiɗe zuwa Fati Washa. A yanzu dai, labarin ya koma kan Alhaji Mainasara (Sadiq Sani Sadiq), wanda ke neman soyayya ta gaskiya ta hanyar ɓoyewa cikin halin talauci. Har ila yau, fim ɗin ya fito da sababbin jarumai mata kamar Firdausi Yahaya, Fatima Hussaini, da Amina Uba Hassan.

Yawancin fitowar fim ɗin na mako guda suna samun kallo sama da miliyan ɗaya.

  1. Manyan Mata

Fim ɗin Manyan Mata shiri ne da ya tattaro jarumai da dama, inda aka nuna yadda wasu mata ke fama da wahalhalu a gidajen aure da sauran matsaloli. A gefe guda, wasu matan sun fito suna ƙoƙarin kare haƙƙinsu da na sauran mata. Shirin ya samu karbuwa sosai saboda darajarsa da kuma sakonnin da yake isarwa.

See also  I was beaten before being allowed to participate in the movie - Khadija Mai Numfashi

Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ne ya shirya fim ɗin, tare da jagorancin daraktoci biyu, Sadiq N. Mafia da Ali Gumzak. A yanzu haka, an kai ga zango na huɗu, kuma fim ɗin yana samun kallo kusan 500,000 duk mako.

  1. Gidan Sarauta

Gidan Sarauta fim ne da aka fara fitarwa a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2023, kuma a yanzu yana ci gaba da jan hankali a zango na uku. Labarin ya mayar da hankali kan soyayya tsakanin yarima da talaka, inda aka samu rikici tsakanin soyayya da sarauta.

Jarumai kamar Umar M. Shareef, Mommee Gombe, Garzali Miko, da Aisha Najamu sun taka rawar gani a cikin fim ɗin. Darakta Ali Nuhu ne ya jagoranci shirin.

  1. Garwashi

Garwashi fim ne da aka fara dora a YouTube a watan Agusta, 2024. An gina labarin ne kan wahalhalun da matan da suka rasa mazansu ke fuskanta. Jaruma Asma’u (Firdausi Yahaya) ta taka rawar gani sosai a cikin fim ɗin.

See also  Fina-Finan Hausa Guda biyar da aka Haska a ƙasashen waje

Marubuciya Fauziyya D. Suleiman ta tsara labarin, yayin da darakta Yaseen Auwal ya bayar da umarni.

  1. Allura Cikin Ruwa

Fim ne da aka shirya kan rayuwar Na’ima (Rukky Ali), wata marainiya da aka gano tana da tarin dukiya. Labarin ya taɓo batutuwan soyayya, ƙarya, da gaskiya. Kamfanin 2Effects ne ya dauki nauyin shirin, yayin da Yakubu Mohammed ya jagoranci shirin. A yanzu ana zango na biyu.

Kammalawa

A bana, Kannywood ta ci gaba da ɗaukar sabbin dabaru wajen shirya fina-finai, wanda hakan ya taimaka wajen dawo da martabar masana’antar. Wannan na nuna cewa Kannywood na kan tafarkin bunkasa domin tabbatar da dorewa da ƙara jan hankalin duniya baki ɗaya.

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X
Join our WhatsApp Channel
Tags: HarsashiKannyWoodLabarinaManyan mata
NgHausa

NgHausa

Related Posts

Kannywood Ta Yi Rashi: Fitaccen Jarumi Malam Nata’ala Ya Rasu Bayan Doguwar Jinya

Kannywood Ta Yi Rashi: Fitaccen Jarumi Malam Nata’ala Ya Rasu Bayan Doguwar Jinya

by NgHausa
November 2, 2025
0

Masana’antar Kannywood ta shiga cikin jimami bayan samun labarin rasuwar shahararren jarumi Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam...

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

by NgHausa
October 29, 2025
0

Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya daga cikin fitattun dattawan masana’antar Kannywood, ya bayyana yadda ya...

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad

by NgHausa
October 28, 2025
0

Jaruma Khadija Muhammad, wacce ta fito a fina-finai irin su Gidan Sarauta, ta bayyana a fili cewa ba ta shiga...

Kannywood: Masana Na Tunanin Komawa Gidajen Gala Bayan Dogaro da YouTube

Kannywood: Masana Na Tunanin Komawa Gidajen Gala Bayan Dogaro da YouTube

by NgHausa
October 5, 2025
0

Masana Kannywood na tattauna yiwuwar komawa haska finafinai a gidajen gala bayan dogon lokaci suna dogaro da YouTube, domin fadada...

Recent Posts

  • Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai
  • Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai
  • Kotun Tarayya Ta Ci Gaba da Shari’ar Nnamdi Kanu Ba Tare da Shi Ba Bayan Zargin Rashin Ladabi
  • ASUU Benin Ta Karyata Sabon Ƙarin Albashi: “Ba Zai Hana Ƙaurawar Malamai Ba

Recent Comments

  1. Yusuf tanko on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
  2. Abdulazeez jibrin on Yadda Zaka Samu Tallafin Kudi a Najeriya (2025): Matakai da Sharuɗɗa
  3. Bashir Gamzaki on COMPLETE RAMADAN TAFSEER 1446/2025 PROF. Isah Ali Ibrahim Pantami
  4. IBB on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
  5. IBB on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”

Archives

  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024

Categories

  • Blog
  • Entertainment
  • Hausa Series
  • KannyWood
  • Labaran Duniya
  • Lafiya
  • Nigeria
  • Nishadi
  • Opportunity
  • Siyasa
  • Sports
  • TAFSEER
  • Wasanni
NgHausa News

© NG Hausa News – 2025

Navigate Site

  • About Us
  • Privacy Policy
  • Terms and Conditions
  • Disclaimer
  • Contact Us

Follow Us

No Result
View All Result
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood

© NG Hausa News – 2025

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
Enable Notifications OK No thanks