INEC Za Ta Fara Sabon Rajistar Masu Zaɓe Gabanin Zaɓen 2027

INEC voter registration 2025, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta fara sabon rajistar masu zaɓe a fadin Najeriya daga wannan watan Agusta, a shirye-shiryen da take yi na babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X (tsohon Twitter) ranar Juma’a, ta sanar da cewa za a fara rajistar ta yanar gizo daga ranar 18 ga watan Agusta.
Kazalika, hukumar ta bayyana cewa za a fara rajistar kai tsaye a ofisoshinta na ƙananan hukumomi da sauran wuraren da aka ware, daga ranar Litinin 25 ga watan Agusta.
INEC ta ce za a gudanar da aikin a kowace rana daga Litinin zuwa Juma’a, tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana.
Ta kuma buƙaci duk ‘yan Najeriya da ba su da rajista da su gaggauta yin rajistar domin samun damar kada ƙuri’a a zaɓukan da ke tafe.
Hukumar ta sake jaddada cewa dole ne mutum ya kasance yana da shekaru 18 ko sama da haka kafin a ba shi damar yin rajistar zaɓe a Najeriya.
INEC Voter Registration 2025