Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya fara karanta hukunci a shari’ar ta’addanci da aka dade ana yi wa jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, a lokacin da ba ya cikin kotu.
Alkali Omotosho ya umarci a ci gaba da shari’ar ba tare da Kanu ba, bayan ya bayyana halayensa a kotu a matsayin marasa ladabi da rashin mutunci.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙin amincewa da sabbin buƙatu uku da lauyoyin Kanu suka gabatar, wadanda kotu ta ce ba su da hujja.
A yayin zaman, Kanu ya katse karanta hukuncin, yana mai jaddada cewa kotu ba za ta iya ci gaba da shari’ar ba saboda bai mika rubutaccen jawabin kare kansa na ƙarshe ba.
Ya ɗaga murya a kotu yana cewa:
“Wace doka ta ce za ku gurfanar da ni bisa doka da ba ta wanzu? Ku nuna min. Omotosho, ina dokar? Duk wani hukunci da aka yanke a nan shirme ne.”
Ya kuma zargi Mai Shari’a Omotosho da son kai, tare da cewa alkalin ba ya fahimtar doka.
Bayan ɗan hutu, tawagar masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Adegboyega Awomolo ta roƙi kotu da ta ci gaba da shari’ar ba tare da Kanu ba saboda hanyarsa ta tada hankali.
Mai Shari’a Omotosho ya bayyana cewa duk da cewa doka ta ba wanda ake tuhuma damar kasancewa a kotu yayin shari’a, amma idan ya dinga tada hankali ko rashin ladabi, kotu na da damar cigaba da shari’ar ba tare da shi ba.
Ya ce:
“Idan wanda ake tuhuma ya nuna rashin mutunci ko ya yi halin da bai dace ba a lokacin shari’a, ana iya ci gaba da shari’arsa ba tare da kasancewarsa ba.”
Ya ƙara da cewa kotun shari’a “haikali ne na Allah”, don haka dole a mutunta ta.
Alkali Omotosho ya ce wannan halin na rashin ladabi daga Kanu ba sabon abu ba ne, domin ya saba nuna irin wannan hali a lokuta da dama a baya.
Ya kuma bayyana cewa Kanu ya bayyana a baya cewa ba zai gabatar da wata kare kansa ba, sannan zaman na ranar Alhamis ɗin da ta gabata domin karanta hukunci da yiwuwar yanke masa hukunci ne.
Bayan umarnin da alkali ya bayar, aka fitar da Kanu daga cikin kotu, sannan Mai Shari’a Omotosho ya ci gaba da karanta hukuncin.

















