Dangote Ya Rage Farashin Litar Mai Zuwa ₦820

Kamfanin matatar man Dangote ya sanar da sabbin sauye-sauye a farashin litar mai, inda ya rage farashin daga ₦840 zuwa ₦820.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Talata, an bayyana cewa wannan saukin naira 20 na da alaƙa da sauyin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Wannan Ba Shine Karo Na Farko Ba
A watan Yuni da ya gabata, kamfanin Dangote ya saukar da farashin lita daga ₦880 zuwa ₦840 — matakin da ya janyo cece-kuce daga ‘yan kasuwa da masu sayar da man fetur.
Tasirin Sauyin Farashin
Gidajen mai kamar MRS, Ardova, da Heyden, wadanda ke da yarjejeniya ta musamman da matatar Dangote, ana sa ran za su daidaita farashinsu bisa sabon tsari.
Martani Daga Masu Ruwa da Tsaki
Raguwar farashin da Dangote ke yi lokaci zuwa lokaci yana yawan haifar da martani daga sauran ‘yan kasuwa, musamman masu shigo da mai daga waje, wadanda ke fuskantar tashi-tsaye wajen farashi da riba.