Nafison fitowa a matsayin masifaffiya a cikin Film inji Fa’iza Abdullahi

Faiza Abdullahi, jarumai dake fitowa a matsayin matar Kofur Audu a shirin Dadin Kowa, ta bayyana haka ne ga mujallar film a lokacin tattaunawar ta da wakilin ta.
Mu fara da jin tarihin rayuwar ki.
FA’IZA: Na farko, suna na Fa’iza Abdullahi. An haife ni ne a cikin Jihar Bauchi, a wani gari da ake kira Jalaf a Ƙaramar Hukumar Damban. A can na yi karatu na girma duk a can. A yanzu dai ban wuce shekara 26 ba, sai kuma a yanzu da na kasance a garin Kano ina gudanar da sana’a ta ta aikin fim.
Shin fim ne ya kawo ki Kano kuma a wane lokacin kika zo?
FA’IZA: To gaskiya, zuwa na Kano zai kai shekara bakwai a yanzu kuma harkar fim ce ta kawo ni Kano, don in ban da ta dalilin fim ban san kowa a Kano ba, ban ma taɓa zuwa ba sai ta sanadin zan yi fim.
Da yake an fi sanin Fa’iza Abdullahi a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ a matsayin matar Kofur Audu, ko kin taɓa yin wani fim ɗin kafin ki fara ‘Daɗin Kowa’?
FA’IZA: Gaskiya ban taɓa yin wani fim ba sai ‘Daɗin Kowa’, don da shi na fara. Ba zan manta ba lokacin da na zo garin Kano haka, ina zuwa Zoo Road akwai wani da na sani wanda shi ne darakta a fim ɗin a lokacin, nakan je na gaishe su, duk da ban ma san shi waye ba a lokacin, sai wata rana ya kira ni ya ce na zo ana nema na zan yi sin ɗaya a wani aiki, to ban ma san yadda abin yake ba sai da na je. To da haka na fara, har aka zo daga baya ake kira na lokaci zuwa lokaci. Kuma lokacin da na fara fitowa a cikin ‘Daɗin Kowa’, a matsayin ‘yar tuwo-tuwo ce mai sayar da abinci, kuma ba mu da gida, ni kaɗai ce a wajen abinci sai masu zuwa su saya.
Shin akwai bambanci tsakanin rayuwar Fa’iza Abdullahi ta zahiri da kuma ta shirin ‘Daɗin Kowa’?
FA’IZA: To akwai bambanci sosai, saboda ka ga dai ita Fa’iza Abdullahi a zahiri ba ta faɗa, sannan tana girmama na gaba da ita da sauran abubuwa na girmamawa. Amma ita Bilkisu a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ ba ta da kunya, ba mu’amala mai kyau, ko gidan su ma ba ta girmama su ba. Haka gidan mijin ta ma ba ta raga wa kowa ba. To amma sai ya kasance mutane a gari suna kallo na a matsayin Bilkisu maimakon su kalle ni a matsayin Fa’iza Abdullahi. Da yawa abin da na fi fuskanta a rol ɗin da nake, sai mutane idan mun haɗu su rinƙa cewa Allah ya ƙara. Abin da nake yi wa Kofur Audu suna jin daɗi saboda macuci ne azzalumi. Wasu kuma suna cewa bai kamata ba, na rinƙa sassauta masa.
Wane rol kika fi so a saka ki?
FA’IZA: Gaskiya duk da a cikin fim babu rol ɗin da ba na takawa, na fi so a saka ni na fito a masifaffiyar mace. Ina son na fito na yi masifa yadda rai na yake so. Don ka ga ko rol ɗin da nake yi a yanzu a cikin fim ɗin ‘Muhalli’ wani rol ne da na fito a matsayin matar aure amma marar mutunci, masifaffiya. Don haka ina son rol ɗin sosai na fito a matar aure marar mutunci, marar tarbiyya. Don haka nake son rol ɗin, don an ba ni dama ina yin masifa yadda rai na yake so, kuma ga ni matar mai kuɗi, ina jin daɗin rayuwa, ga kuma ina zuba masifa. Don haka ina jin daɗi sosai da wannan rol ɗin.