Hukumar Ba da Lamunin Ilimi ta Najeriya (NELFUND) ta sanar da shirin fadada tsarin bayar da lamunin dalibai domin ya hada da masu koyon sana’o’i da horon fasaha a fadin kasar.
Manajin Daraktan NELFUND, Akintunde Sawyerr, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Hukumar Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.
Sawyerr ya ce wannan mataki ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Tarayya na kara bunkasa ilimi da basirar matasa domin samar da cigaban kasa mai dorewa.
Ya kara da cewa shirin na nuni da kudirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na inganta habakar dan Adam ta hanyar bai wa dukkan matasa damar samun ilimi — ba wai na jami’a kadai ba har ma da na sana’o’i.
“Ba malamai masu falsafa kadai ake gina kasa da su.
“Yana da matukar muhimmanci mu samu mutane masu iya amfani da hannayensu, kuzari, karfi da fasaha wajen aiwatar da kyawawan dabarun da suka fito daga cibiyoyin ilimi,” in ji shi.
Sawyerr ya bayyana cewa tun bayan kafuwar NELFUND, an fi mayar da hankali ne kan tallafa wa daliban makarantu na gaba da sakandare, amma yanzu ana shirin bude kofar samun lamuni ga masu koyon sana’o’i da fasaha a cibiyoyin horo a duk fadin kasar.
A cewarsa, matakin cigaban Najeriya na gaba yana bukatar daidaito tsakanin ilimi na rubutu da kuma na fasaha.
“A NELFUND muna da hurumin tallafawa shirin koyon sana’o’i.
“Ba mu fara aiwatar da shi ba tukuna, amma ina da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tabbatar da cewa an fadada tsarin basirar matasa yadda ya kamata.
“Ma’aikatar Harkokin Matasa tana da shirye-shiryen horo; Ma’aikatar Ilimi tana kan batun basira; sannan Ma’aikatar Tattalin Arzikin Dijital tana koyar da IT da soft skills.
Ya ce kusan bangarori da dama na gwamnatin tarayya suna da alhakin horar da matasa da basirar aiki.
“Na yi imanin cewa injiniya mai iya gina abu ya fi injiniya mai iya zane kawai.
“Matakin da Najeriya take yanzu shi ne matakin ‘design, build and operate’ — wato zayyana, ginawa da gudanarwa,” in ji shi.

















