KannyWood

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

A kwanakin nan, wasu daga cikin tsoffin jarumai na masana’antar Kannywood kamar su Ummi Nuhu sun bayyana damuwarsu kan yadda rayuwa ta sauya musu bayan tsawon lokaci suna cikin farin jini da daukaka.
A cewar su, duk da irin shaharar da suka samu a baya, yau al’amura sun juya musu baya.

Ɗaya daga cikin jarumai da ta yi fice a wancan lokaci ita ce Ummi Nuhu, wadda ta shahara sosai daga shekarar 2000 zuwa 2015. A wannan lokaci, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun jarumai a karkashin jagorancin Ali Nuhu, tana fitowa a fina-finai kamar Al’amari, Fil’azal, Zo Mu Zauna da Rabin Jiki, a kamfanin FKD.

Fice da Bacewa Daga Fagen Fim

Ummi Nuhu ta fito daga iyayen asalin Bunkure, Kano, amma aka haife ta a Kaduna.
Daga baya, sai ta ɓace daga harkar fim ba tare da bayani sosai ba.
A cikin hira da Hadiza Gabon a shirin Gobon’s Room Talk Show da kuma wata hira da BBC Hausa, Ummi ta bayyana dalilan da suka sa ta daina fitowa a fim.

See also  Dawowar Tsofaffin Jaruman Kannywood: Yadda Finafinai Masu Dogon Zango Suka Farfaɗo da Su

Ta ce a wancan lokaci babu wani furodusa da zai shirya fim ba tare da ya nemi ta fito ba. Ta samu kuɗi, daukaka da tarin masoya a ko’ina. Sai dai kuma, kuskure a rayuwa da rashin tsari suka jawo ta rasa komai.

Hatsari da Canjin Rayuwa

Babban abin da ya fi jefa ta cikin koma-baya shi ne hatsarin mota da ta yi, wanda ya jawo mata karaya huɗu a ƙafa, bugu a kai, da raunuka masu tsanani a fuska.
Wannan hatsari ya tilasta mata tsawon lokaci tana jinya har ma ta manta da abubuwa da dama a rayuwarta.

Duk da cewa babu wanda ya ɗauki nauyin jinyarta gaba ɗaya, Ummi ta ce abokan sana’a sun rika ziyarta don yi mata jaje. “Ni ce na ɗauki nauyin jinyata saboda a lokacin ina da abin da zai iya tallafa min,” in ji ta.

See also  Jerin Fina-Finan da Suka Yi Tashe a Kannywood 2024

Da-na-sani Kan Rashin Aure

Ummi ta bayyana cewa babban abin da ta fi da-na-sani a rayuwa shi ne rashin yin aure.
A cewarta, da ta yi aure, da Allah ya ba ta ‘ya’ya waɗanda za su kula da ita yanzu da kuma lokacin tsufarta.
Ta yi fatan samun damar yin aure kafin rayuwarta ta kai ƙarshe.

Shawara Ga Matasa Masu Tasowa a Kannywood

A ƙarshe, tsohuwar jarumar ta shawarci matasa, musamman mata masu tasowa a Kannywood, da su yi tunani mai nisa.
Ta ce ya zama wajibi su saka hannun jari a harkokin kasuwanci da za su samar musu da dogaro da kai bayan lokacin daukakarsu ya wuce.
“Lokaci zai zo da ko da kin yi fice sosai, komai zai gushe, ki zama kamar ba ki taɓa shahara ba,” in ji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks