KannyWood

Jaruman Kannywood da suka rasu a 2024

Har yanzu masana’antar Kannywood da masu bibiyarta suna jimamin rasuwar fitaccen mawaƙi El-Mu’az Birniwa, wanda ya rasu a daren Laraba, 4 ga Disamban 2024 a Kaduna.

Rasuwar El-Mu’az ta yi matuƙar girgiza masana’antar Kannywood da ma masoyansa. Hakan ya faru ne saboda yanayin mutuwarsa ta fuju’a, wanda ke sanya jimami ya ɗauki lokaci sosai, musamman ma idan irin wannan mutuwar ta farat-ɗaya ce.

El-Mu’az ya shiga jerin fitattun ‘yan masana’antar da suka yi rasuwar fuju’a, irin su Saratu Daso, Mustapha Waye, da darakta Aminu S. Bono. Wadannan mutane sun bar ƙaƙƙarfan gurbin da ba za a manta da shi ba.

Rasuwar wasu fitattun ‘yan Kannywood a 2024

A ƙarewar shekarar 2024, rahotanni sun tattara sunayen wasu fitattun jarumai da suka rasu cikin shekarar, waɗanda suka bar babban gibi a masana’antar. Ga su kamar haka:

Fatima Sa’id (Bintu Dadin Kowa)

A ranar Lahadi, 11 ga Fabrairun 2024, jaruma Fatima Sa’id, wadda aka fi sani da Bintu Dadin Kowa, ta rasu. Jarumar ta yi fice a shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24, inda aka yaba nata saboda natsuwarta da ƙwarewarta a aikinta. Ta rasu ne sakamakon rashin lafiya, kuma mutuwarta ta girgiza abokan aikinta da masoyanta.

Saratu Giɗaɗo (Saratu Daso)

Ita ma Saratu Giɗaɗo, wadda aka fi sani da Saratu Daso, ta rasu ne a ranar Laraba, 9 ga Afrilu, bayan ta kammala shirye-shiryen sallah. An yi sahur da ita, amma ta rasu a safiyar ranar.

Daso ta shahara a masana’antar Kannywood wajen taka rawar gani a finafinai da kuma yin barkwanci. Mutuwarta ta fuju’a ta yi matuƙar girgiza masana’antar da masoyan finafinan Hausa a duniya.

Fatima Usman (Fati Slow Motion)

Tsohuwar jaruma Fatima Usman, wadda aka fi sani da Fati Slow Motion, ta rasu a watan Mayu 2024 a yankin Ouaddai na ƙasar Chadi, kuma a can aka binne ta. Duk da cewa ba ta yawan fitowa a finafinai a lokacin rasuwarta, amma ta yi suna a shekarun farko-farko na habbakar Kannywood. A baya-bayan nan, ta shahara a shafukan sada zumunta, inda ta bar kalmar da ta fi amfani da ita – kebura.

Sulaiman Alaqa

A ranar 22 ga watan Yuli 2024, jarumin Kannywood Sulaiman Alaqa ya rasu. Shi ne mahaifin jarumar Dadin Kowa, Bintalo. Duk da cewa ba ya cikin jaruman da suka yi fice sosai, ya taka rawar gani wajen gina masana’antar tun yana matashi.

El-Mu’az Muhammad Birniwa

Mawaƙi El-Mu’az Birniwa, wanda ya fito daga jihar Jigawa amma ya yi rayuwa a Kaduna, ya rasu ne yayin shagulgulan taya abokinsa, Auta Waziri, murnar aure. A cewar masoyansa, babban abin da ya dame shi kafin rasuwarsa shi ne rashin cika alkawari. Rasuwar El-Mu’az ta ƙara bayyana rashin tabbas na rayuwa, inda ta bar ‘yan masana’antar cikin baƙin ciki mai tsanani.

Wannan shekarar ta kasance mai ɗauke da babban rashi a masana’antar Kannywood. Wadannan fitattun jarumai da mawaƙa sun bar babban gurbi da za a dade ana jin rashin su.

Allah ya jikansu da rahama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button