Tsohon kwamishinan yada labarai na Jihar Anambra a zamanin Gwamna Willie Obiano, C-Don Adinuba, ya karyata jita-jitar mutuwar tsohon gwamnan, inda ya tabbatar da cewa Obiano yana raye, cikin koshin lafiya, a birnin Houston na ƙasar Amurka, inda yake zaune a halin yanzu.
A kwanakin baya ne aka yayata a shafukan sada zumunta cewa Obiano, wanda ya yi gwamna daga 2014 zuwa 2022, ya rasu a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.
Cikin hirar wayar tarho da ya yi da wakilinmu a ranar Juma’a, Adinuba ya bayyana rahotannin da ake yadawa a matsayin “magana mai tayar da hankali” wadda kuma “ba ta da tushe”, tare da jaddada cewa tsohon gwamnan yana nan da rai lafiya lau tare da iyalinsa a Amurka.
Ya ce, “’Yan jarida sun yi ta tambayata wasu muhimman tambayoyi, tare da jiyo wata mummunar jita-jita game da mutuwar tsohon Gwamna Willie Obiano. Wannan jita-jita karya ce. Na yi magana da tsohon gwamnan da kansa, tare da wasu daga cikin iyalansa, mintuna kaɗan da suka wuce. Yana cikin koshin lafiya a Houston, Amurka, inda yake zaune.”
Ya ƙara da cewa, “Ba gaskiya ba ne rahoton da ke cewa yana Landan ko kuma an kwantar da shi a asibiti. Obiano ba ya Landan, ba a kwantar da shi a asibiti ba. Yana da ƙarfi, cikin koshin lafiya, yana harkokinsa a Amurka. Ku yi watsi da jita-jitar — ba ta fito daga wani sahihin tushe ba. Don Allah a sani wannan labari ƙarya ne; Obiano yana raye.”
Adinuba ya roƙi jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni da ba su da tabbataccen asali.
Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Tony Nezianya, shi ma ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu wani sahihin bayani da ke tabbatar da mutuwar Obiano ba.
Ya ce, “Ba zan iya tabbatar da wannan ba, ban samu wani labari na haka ba.”
Willie Obiano ya shugabanci Jihar Anambra a matsayin gwamna daga 2014 zuwa 2022, inda ya gaji Peter Obi, sannan daga bisani ya miƙa mulki ga gwamna mai ci yanzu, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, a watan Maris 2022.
Asalin Obiano dan asalin garin Aguleri ne, a ƙaramar hukumar Anambra East, kuma an haife shi ne a ranar 8 ga watan Agusta, 1955.
A halin yanzu dai, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) na ci gaba da bincikensa kan zargin almundahanar Naira biliyan huɗu (N4bn) da ake masa.

















