Siyasa
Har yanzu Kwankwaso bai rufe ƙofar tattaunawa da APC ba – Abdulmumin

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Ce APC Na Buɗe Ga Kwankwaso
Ɗan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa har yanzu jam’iyyar APC ta na buɗe ƙofa ga tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, idan ya yanke shawarar komawa jam’iyyar mai mulki.
Abdulmumin ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV da yammacin ranar Laraba.
“Dangane da abin da ya shafi APC, ya (Kwankwaso) nanata cewa ƙofar tattaunawa har yanzu a buɗe take. Komai na iya yiwuwa,” in ji shi.
Ɗan majalisar ya kuma ƙara da cewa, bai ga wani dalili da zai hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu yin tazarce ba idan lokaci ya yi.
A kwanakin baya ma, Kwankwaso da kansa ya tabbatar da wannan yiwuwar a wasu tattaunawa da ya yi da manema labarai.