Kotun Tarayya Ta Bukaci A Dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin cewa a dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan zuwa majalisar dattawa bayan dakatar da ita na tsawon watanni shida.
A cikin hukuncin da ta yanke, mai shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa Natasha ta yi tsauri sosai, la’akari da yadda take da hakkin wakiltar mazabarta.
Majalisa Na Da Iko – Amma Ba Har Ta Tauye Haƙƙi
Kotun ta ce duk da cewa majalisar dattawa na da damar ladabtar da duk wani ɗan majalisa da ya aikata laifi, ba ta da ikon ɗaukar matakin da zai hana ɗan majalisar gudanar da ayyukan wakilci. Ta kara da cewa:
“Ƴan majalisa suna da kwanaki 181 don zama a kowanne zangon mulki. Dakatar da Natasha na watanni shida kamar hana ta wakiltar mazabarta ne tsawon kwanaki 180.”
Akpabio Bai Yi Laifi Ba – In Ji Kotu
Kotun ta kuma wanke shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, daga zargin tauye hakkin Natasha. Ta ce lokacin da ya hana ta yin magana a zauren majalisa, ba ta kasance a kujerar da aka ware mata ba, don haka matakin da ya dauka ya dace.
An Ci Natasha Tarar Miliyan Biyar
Tun da farko, kotun ta ci tarar Sanata Natasha Akpoti naira miliyan biyar saboda raina kotu, inda ta karya dokar da ta hana bangarorin biyu magana da kafafen watsa labarai game da shari’ar.
Kotun ta kuma bukace ta:
- Nemi afuwa a jaridu guda biyu.
- Rubuta bayani na hakuri a shafinta na Facebook cikin kwanaki bakwai.
Asalin Rikicin
A watan Maris ne aka dakatar da Natasha daga majalisa, bayan da ta zargi shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio, da cin zarafi na lalata. Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce da kuma kiran da dama na ganin an bi hanyar doka.