KannyWood

Fina-Finan Hausa Guda biyar da aka Haska a ƙasashen waje

Haska Finafinan Hausa a Duniya: Nasarori da Ci gaban Kannywood

Masu bibiyar masana’antar Kannywood suna ci gaba da bayyana farin cikinsu kan gagarumar nasarar da aka samu wajen haska finafinan Hausa a ƙasashen duniya, musamman a ƙasar Saudiyya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake murnar zaɓen fim ɗin “Mai Martaba”, wanda zai wakilci Najeriya a gasar karrama finafinai ta duniya—Oscars karo na 97 a Amurka.

Finafinan Hausa da Aka Haska a Ƙasashen Waje

Baya ga gasar Oscars, fim ɗin Mai Martaba ya samu shiga gasar karrama finafinai ta Septimius a birnin Amsterdam, Netherlands. Haka kuma, an haska wasu finafinai da suka ja hankalin duniya. Sai dai, hakan ya janyo tambayoyi daga wasu masu sharhi a masana’antar—me yasa finafinan Hausa ba su da yawa a manyan kasuwannin duniya?

Wasu Finafinan Hausa da Aka Haska a Ƙetare

1. Jalil

Fim ɗin Jalil ya shafi labarin iyali, inda Zahrah (Maryam Booth) da Yusuf (Yakubu Mohammed) ke fafutukar samun Naira miliyan 33 domin yi wa ɗansu Jalil tiyatar zuciya. Sai dai, a tsakiyar yunƙurin neman kuɗin, an yi garkuwa da mahaifiyar Yusuf.

An haska fim ɗin a ranar 22 ga Maris, 2020, a Plaza Theatre, Atlanta, Amurka. Kamfanin Noless Studios ne ya ɗauki nauyin shirin, tare da umarnin Leslie Dapwatda.

2. Nanjala

Nanjala fim ne da ya haɗa manyan jaruman kudancin Najeriya kamar Enyinna Nwigwe, Nancy Isime, Segun Arinze, Sola Sobowale, tare da fitattun jaruman Kannywood kamar Ali Nuhu da Rabiu Rikadawa.

Fim ɗin ya bi sawun rayuwar ƴar jarida, wato Nanjala (Nancy Isime), kuma an haska shi a Turkiyya da Amurka kafin daga bisani a fara nunawa a Najeriya. Kabiru Jammaje da Abubakar Bashir Maishadda ne suka shirya, yayin da Ali Nuhu ya bayar da umarni.

3. Mamah

Fim ɗin Mamah ya ɗauki hankalin mutane musamman a ƙasar Saudiyya, inda aka haska shi a ranar 9 ga Disamba, 2024, a Red Sea Culture Square.

Abdul Amart Maikwashewa da Rahama Sadau ne suka shirya fim ɗin, yayin da Toka Mcbaror ya bayar da umarni.

4. Mai Martaba

Wannan shi ne fim ɗin da aka zaɓa domin wakiltar Najeriya a gasar Oscars 2025. An shirya shi a jihar Katsina, inda ya bayyana tarihin kasuwancin dauri tsakanin ƙasashen Afirka.

Fim ɗin ya samu sahalewar hukumar tantance finafinai ta Najeriya, sannan an tantance shi a Amurka. Ana sa ran za a karrama finafinan da suka samu shiga gasar a ranar 2 ga Maris, 2025. Prince Daniel ne ya shirya fim ɗin kuma ya bayar da umarni.

5. Kakah

Kakah fim ne da ke bayyana matsalar garkuwa da mutane da ayyukan ƴan bindiga a garin Duma.

Jarumar fim ɗin, Kaka, ta taso a ƙauye, amma saboda damuwar da take fuskanta, ta yanke shawarar komawa birni domin samun ilimi da fatan taimakon ƙauyenta.

Fim ɗin ya samu lambar yabo ta kwalliya mafi kyau a gasar TAFF 2024 da aka gudanar a Amurka, tare da wasu kyaututtuka da dama.


Shin Kannywood na Matsowa Gab da Manyan Masana’antu?

Yayin da ake ci gaba da samun finafinan Hausa a gasar finafinai ta duniya, tambayar da wasu ke yi ita ce: me yasa finafinan Hausa ba su da yawa a manyan kasuwannin duniya duk da ƙarfin harshen Hausa?

Wannan ci gaba na nuna cewa masana’antar Kannywood na ƙara samun shahara, kuma yana da kyau a ƙara ƙoƙari wajen inganta tatsuniya, rubutun labari, da fasaha domin finafinan Hausa su shiga manyan kasuwanni kamar Hollywood da Bollywood.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button