Tsoffin Jiga-Jigan Gwamnatin Buhari Sun Koma ADC: Sabon Kalubale Ga Gwamnatin Tinubu?

Tsoffin jiga-jigan gwamnatin Buhari sun fara bayyana goyon bayansu ga sabuwar haɗakar jam’iyyar ADC. Wannan ya janyo tambayoyi da dama game da matsayinsu kan gwamnatin Bola Tinubu. A wani taron siyasa da aka yi a ranar Laraba, wasu fitattun ‘yan siyasa daga APC da jam’iyyun adawa suka sanar da haɗuwa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC domin kalubalantar gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Dalilin Ficewarsu Daga APC
Tsoffin mukarraban gwamnatin Buhari, musamman daga tsohuwar jam’iyyar CPC, sun bayyana rashin jin daɗinsu da yadda ake tafiyar da mulki a yanzu. Wasu daga cikinsu sun ce ba a damawa da su a sabuwar gwamnatin Bola Tinubu. Kodayake wasu sun nisanta kansu daga wannan ra’ayi, har yanzu akwai alamun cewa ƙin jin daɗin ya fara fitowa fili.
Masanin Siyasa Ya Yi Sharhi
Malam Kabir Sufi, masanin kimiyyar siyasa daga Kano, ya ce wannan sauyin matsayi ba sabon abu ba ne. A cewarsa, dama wasu daga cikin tsoffin abokan Buhari ba su goyi bayan Tinubu a zaɓen 2023. Yanzu adawar ta fito fili. Ya ce akwai alamun wasu daga cikinsu sun fita daga jam’iyyar domin ƙirƙirar wata sabuwar hanya don kalubalantar gwamnati mai ci.
Fitattun Mutane Da Suka Koma ADC
- Abubakar Malami – Tsohon ministan shari’a. Ya sanar da ficewa daga APC, ya ce a shirye yake ya yi aiki da ADC don kawar da gwamnatin Tinubu.
- Rotimi Amaechi – Tsohon ministan sufuri kuma na biyu a zaɓen fidda gwani na APC. Ya bayyana niyyarsa ta goyon bayan haɗakar da za ta kalubalanci Tinubu.
- Rauf Aregbesola – Tsohon ministan harkokin cikin gida. Ya zama sakataren haɗakar ADC.
- Nasir El-Rufai – Tsohon gwamnan jihar Kaduna. Ya sanar da ficewa daga APC kuma ya ce ya sanar da Buhari wannan matakin nasa.
- Solomon Dalung – Tsohon ministan matasa da wasanni. Ya sha sukar gwamnatin Tinubu kan yadda take tafiyar da lamuran talakawa musamman a arewa.
- Air Vice Marshal Abubakar Sadiq (Rtd) – Tsohon hafsan sojin sama. Ya shiga siyasa bayan ritaya, kuma yanzu yana cikin haɗakar ADC.
- Abubakar Bawa Bwari – Tsohon ministan ma’adinai a lokacin Buhari. Shi ma yana cikin sabuwar haɗakar.
- Muhammad Hassan Abdullahi – Tsohon ministan kimiyya da muhalli. Ya kasance ɗan siyasa daga jihar Nasarawa kuma yanzu yana goyon bayan ADC.
- Lauretta Onochie – Tsohuwar mai ba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta. Ta bayyana a taron ADC tare da sauran jiga-jigan haɗakar.
Martanin Jam’iyyar APC
Jam’iyyar APC ta ce wannan matakin ba sabon abu ba ne. A cewar sabon shugaban riko na jam’iyyar, Ali Bukar Dalori, waɗanda suka fice suna hakan ne kawai saboda ba su samu muƙamai ba a gwamnatin Tinubu. Ya ƙara da cewa sabuwar haɗakar ba ta razana APC.
Tsoffin ministoci sun koma ADC, Zaben 2027 Nigeria, Tinubu vs ADC, Malami da Amaechi a ADC, Jiga-jigan Buhari sun fice daga APC, Abubakar Malami ADC, Amaechi kalubalanci Tinubu, El-Rufai da Aregbesola sun bar APC